Labarai

An harbe Wani Mawaki Dan Afirka Ta Kudu (AKA) A Birnin Durban

An harbe daya daga cikin fitattun mawakan rap na Afirka ta Kudu, wanda aka fi sani da AKA, a birnin Durban da ke gabar teku, tare da wani abokin shi, kamar yadda dangin shi suka bayyana a ranar Asabar.

An kashe Kiernan Forbes ne tare da babban abokin shi, mai dafa abinci kuma dan kasuwa Tebello ‘Tibz’ Motsoane yayin da suke kan hanyar su ta zuwa wurin da motar su take ajiye daga wani gidan cin abinci.