Al'umma

An Garzaya Da Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari Zuwa Asibiti

An garzaya da Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari asibitin Abuja bayan ta samu cikas a kafa a karshen mako.

Kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN da SaharaRepoters suka ruwaito, majiyoyi sun ce Aisha “ta fadi kasa ta samu targaɗe a kafa” amma cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru har yanzu basu kammala ba a lokacin da ake gabatar da wannan rahoton, kuma ba a bayyana sunan asibitin da aka kai ta ba.

A cewar rahoton, a daren Lahadi ne ake zaton uwargidan shugaban kasar za ta shirya liyafar daurin aure, domin karrama Bilkisu Rimi, diyar jakadan Najeriya a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Mohammed Rimi, a fadar shugaban kasa.

Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa bai amsa tambayoyi ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton.

Advertisement