Siyasa

An ga Kwankwaso ba sanye da jar hula ba a karon farko [Hoto]

Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, shi ne jagoran jam’iyyar PDP a Kano wanda aka fi sani da Kwankwasiyya.

Kwanan nan, an ga Kwankwaso ba tare da jan hula ba a ziyarar da ya kai Jami’ar Sharda, kasar Indiya.

Idan dai ba a manta ba Kwankwanso na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP ne domin ya ci gaba da harkokinsa na siyasa.

Advertisement

Wannan shi ne babban dalilin da yasa ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a yunkurin shi na ganin ya kammala zuwan shi jam’iyyar da ake sa ran zai yi amfani da shi wajen neman shugabancin kasar nan a 2023.

A cikin Hotuna: Daga daman shi shine Farfesa Gaurav Saini, daga hagunsa, Farfesa Rameshwar Adhikar da sauran ƙwararrun malamai a lokacin nasararsa na Final viva gabatarwa.

Advertisement