Laifuku

An Daure Alkalan Kotun Shari’ar Musulunci 8 Bisa Laifin Murkushe Miliyan N99 Na Gadon Marayu

Alkalai takwas da ma’aikatan Hukumar Shari’ar Musulunci 7 aka tsare a gidan yari bisa zargin karkatar da naira miliyan N99 mallakar marayu a jihar Kano.

Wata kotun majistare da ke Kano karkashin jagorancin Mustapha Sa’ad Datti, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare su a ranar Alhamis din da ta gabata, biyo bayan tuhumar karkatar da naira miliyan N99 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta gurfanar da mutane 15 a gaban kotun.

Alkalin kotun Mai shari’a Datti ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari, a ci gaba da zama na gaba.

Advertisement

Wadanda ake tuhumar sun hada da Gazzali Wada, Sani Ali, Yusuf Abdullahi, Sani Uba Ali, Bashir Baffa, Hadi Tijjani Mu’azu, Alkasim Abdullahi da Mustafah Bala.

Sauran wadanda ake tuhuma da ke tsare a gidan yari na Najeriya sun hada da Abdullahi Sulaiman Zango, Bashir Ali Kurawa, Jaafar Ahmad, Adamu Balarabe, Aminu Abdulhadi, Garba Yusuf, da Usaina Imam.

Advertisement