Siyasa

An dauki siyasa da zafi: Ortom ya caccaki jami’an tsaro akan hana shi ganin Osinbajo

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana rashin jin dadin shi da jami’an tsaro suka hana shi ganin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a Makurdi, babban birnin jihar.

An hana gwamnan shiga sansanin sojojin saman Najeriya (NAF) dake babban birnin jihar domin tarbar mataimakin shugaban kasar dake kan hanyar shi ta zuwa Jalingo a jihar Taraba, domin gudanar da taron babbar jami’ar tarayya dake Wukari.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Ortom, Nathaniel Ikyur ya fitar, Ortom yace ya samu wasika daga fadar gwamnatin jihar cewa Osinbajo zai bi ta Makurdi zuwa jihar Taraba domin gudanar da taron.

Advertisement

Ya bayyana halin jami’an tsaron da suka hana shi ganin mataimakin shugaban kasa a matsayin siyasa ta wuce gona da iri.

Ortom yace: “Abin takaici, da suka isa babbar kofar rundunar sojojin sama, jami’an tsaro dake kofar shiga sun ce ba za’a bari ayarin gwamnan ya shiga ba, domin a cewar su, ba’a sanar da su ziyarar da gwamnan ya kai sansanin domin karbar bakuncin mataimakin shugaban kasa ba.

Gwamnan yayi mamakin dalilin da ya sa jami’an sojin sama a jihar da shine babban jami’in tsaro na jihar su yi masa hakan.

“Ya sha alwashin kai rahoton lamarin ga mataimakin shugaban kasa domin daukar matakin da ya dace, yana mai jaddada cewa akwai banbanci tsakanin siyasa da mulki.

Advertisement