Laifuku

An Cafke Yan Kungiyar Tsafi 9 Masu Yanka Sassan Jikin Mutane A Borno

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta kama wasu gungun mutane tara masu tsafi da ake kira “Karangiya” wadanda suka kware wajen yanke sassan jikin wadanda suka fada tarkon su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan, Abdu Umar, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, ya ce jami’an rundunar sun kama su ne a ranar 16 ga Disamba, 2022.

Kanun labaran ya haifar da ra’ayoyi daban-daban a tsakanin masu amfani da Facebook. Ku karanta wasu ra’ayoyin ‘yan Najeriya da suka yi sharhi.

Advertisement
Advertisement