Laifuku

An Cafke Dattijo Mai Shekaru 75 Bisa Zargin Yiwa Jikanya Mai Shekaru 6 Fyade

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta cafke wani dattijo mai shekaru 75, Musa Gambo, da ake zargi da yiwa jikanyar shi mai shekaru shida fyade a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar Jigawa, Cif Sufeto Adamu Shehu ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST.

Yace an kama wanda ake zargin ne bayan rahoton wani ma’aikacin jin dadin jama’a da ya samu kiran gaggawa daga wani abokin ‘yan uwan wanda abin ya shafa yace ta kama wadda ake zargin da hannu a lokacin da ta kai wa kakan yarinyar ziyara.

Adamu yace jami’an NSCDC sun kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba a Gandun Sarki Quarters, Malam Madori LGA, a hannun jami’an NSCDC da misalin karfe 1:00 na rana bisa zargin aikata laifin fyade ga wata yarinya ‘yar shekara shida wadda jikanyar shi ce.

Kamar yadda shedun gani da ido Malama Maimuna ta bayyana, ta kama tsohon ne tare da yarinyar a cinyar shi yayin da yake lalata da ita a dakin shi.

“Nan da nan na sanar da kakar yarinyar da ta garzaya dakin kuma ta ga haka,” in ji ta.

CSC Adamu yace yarinyar da abin ya shafa ta kuma tabbatar da cewa wanda ake zargin ya ci zarafin ta da dama wanda ya saba ba ta alewa sannan kuma yayi mata barazanar kada ta fadawa kowa.

Wani rahoton likita da aka samu daga Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa (SARC) da ke Babban Asibitin Dutse ya nuna alamun cin zarafi da aka yi mata saboda karyewar hushinta. Shi ma wanda ake zargin ya amsa laifin shi tare da danganta shi da aikin shaidan. A cewar Adamu, za a gurfanar da shi a gaban kotu idan aka kammala bincike.

Jaridar Daily Post da sauran jaridu ne suka fara wallafa wannan labarin: https://dailypost.ng/2022/11/20/grandpa-75-arrested-over-alleged-rape-of-grandniece-6-in-jigawa/

Advertisement