An Bankaɗo Polytechnics 16 Da Ba Bisa Ƙa’ida Ba, Duba Idan Wacce Kake Halarta Ba Ta Cikin Su

Daliban da suka samu shaidar difloma a cibiyoyin 16, a cewar hukumar, ba za a bar su su cigaba da karatun su ba, samun aikin yi, ko kuma a hada su da tsarin dole na masu yiwa kasa hidima.

A wani rahoto da hukumar ta NBTE ta gabatar wa manema labarai a ranar Asabar, ta ce za ta hada kai da jami’an tsaro domin rufe haramtattun cibiyoyin.

Wasu daga cikin cibiyoyin da abin ya shafa sun hada da Rufus Giwa Polytechnic, Owo (cibiyoyin karatu na Ibillo da Ekiti); Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, BUK; Jami’ar Ibadan Consultancy Services, Ladoke Akintola Technology, Ogbomosho; Jami’ar Jihar Kwara, Cibiyar Nazarin Malete; Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya ta Awgu, Awgu; Eastern Polytechnic, Fatakwal (Cibiyoyin Nazarin Abuja da Madalla; Interlink Polytechnic, Ijebu-Jesa (Cibiyoyin Nazarin Nyanya da Gwagwalada); da Oke Ogun College of Management Science and Technology, Iseyin.

Sauran su ne First Mark Innovative School of Technology, Ado-Ekiti (Rufus Giwa Study Centre); Delight College of Health Science and Technology, Minna; Makarantar Fasaha ta Jama’atu, Zariya; Kanam Unity College of Health Technology, Dengi; Makarantar Fasaha ta Lafiya ta Savannah, Wudil; Kwalejin Kiwon Lafiya ta Owoseni, Ijesa-Isu Ekiti; Kwalejin Kudancin Maritime, Uwheru, Ughelli; Wolex Polytechnic, Ediene Ikot Obio Imo; Ibeku Polytechnic, Ibeku; da Atlas Polytechnic, Uzuakoli.

Hukumar ta lura cewa cibiyoyin ba su karbi lasisin aiki daga Gwamnatin Tarayya ba kuma suna gudanar da ayyukan su ba bisa ka’ida ba.

Hukumar ta NBTE ce ke da alhakin lura da masana’antar kere-kere, fasahar kere-kere da cibiyoyi masu kirkire-kirkire.