Siyasa

Amurka ta sanar da kakabawa jami’an Somaliya takunkumi akan jinkirta zabe

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed da firaminista Mohamed Hussein Roble

Gwamnatin Amurka ta ba da sanarwar hana jami’ai da daidaikun jama’a na kasar Somaliya takardar izinin shiga kasar, inda ta zarge su da “raguza tsarin dimokuradiyya a Somaliya”, bayan wani jinkirin da aka samu a zaben yan majalisar dokokin kasar.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a ranar Juma’a, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace an sanya takunkumin “domin kara daukar nauyin ayyukansu na kawo cikas.”

An sanar da takunkumin ne sa’o’i kadan bayan shugabannin Somaliya sun tsawaita zaben yan majalisar zuwa ranar 15 ga Maris bayan kasa kammala su a ranar 25 ga Fabrairu.

Advertisement

Blinken yace “Jinkirin da aka samu wajen kammala zaben Somaliya yana haifar da rashin zaman lafiya a siyasance, da yin barazana ga nasarorin tsaro, da kuma kawo cikas ga cigaban tattalin arziki.”

Advertisement