Siyasa

Amurka ta haramtawa Kamfanonin ta da ɗai-ɗaikun mutane hulda da babban bankin Rasha

Babban bankin Rasha

Gwamnatin Biden ta ba da umarnin gaggawa a ranar Litinin na hana kamfanonin Amurka da ɗai-ɗaikun mutane yin kasuwanci tare da Babban Bankin Rasha, Ma’aikatar Kuɗi da Asusun Taimako na Ƙasar Rasha.

Takunkumin da aka sanar shine don tabbatar da cewa tattalin arzikin Rasha “ya koma baya idan shugaba Putin ya yanke shawarar cigaba da mamaye Ukraine,” inji wani babban jami’in Amurka da yayi magana da manema labarai a safiyar Litinin.

“Muna da kayan aikin da za mu ci gaba da yin hakan,” inji jami’in, da yake magana kan yanayin boye sunansa.

Advertisement

Da aka tambaye shi ko an daskarar da duk kadarorin hukumomin Rasha da aka sanya wa takunkumi sakamakon sabon matakin, jami’in ya ce: “Idan wata cibiyar hada-hadar kudi ta Amurka tana da kadarorin Babban Bankin Rasha, ba za su iya yin komai da su ba. Sun makale a wannan cibiyar.”

Advertisement