Tsaro

Amurka ta ce sojojin Rasha sun ci ‘kusan kashi 100’ wajen mamaye Ukraine

Amurka ta fada jiya Laraba cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin “a shirye yake kamar yadda zai iya” don mamaye kasar Ukraine, tare da kusan kashi 100 na sojojin da suka kasance a wurin.

“Mun tantance a yau cewa yana kusan kashi 100 cikin 100 na dukkan dakarun da muke tsammanin zai shiga cikin ƙasar. Yana kusa da kashi 100 cikin 100,” ilwani jami’in tsaron Amurka ya fadawa manema labarai.

Jami’in yace kashi 80 cikin 100 na sojojin da aka kiyasta fiye da 150,000 na Rasha dake kan iyakar Ukraine suna cikin “guraren shirye-shiryen” da suka bazu wajen kai hare-hare a cikin yan kilomita kadan daga kan iyaka.

Advertisement

“A shirye yake kamar yadda zai iya,” inji jami’in. “Ko sun tafi ko a’a da gaske ya rage ga Mista Putin. Za su iya tafiya a kowace sa’a yanzu.”

Advertisement