Siyasa

Amsar Da Tinubu Ya Bayar Da Aka Tambaye Shi Dalilin Da Yasa Bai Bayyana Hanyoyin Samun Kuɗin Shi Ba

A kwanakin baya ne BBC ta yi hira da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Ahmed Tinubu, inda yayi magana kan burin whi na shugaban kasa da kuma shirin shi ga kasar idan ya zabe shi.

A yayin tattaunawar, mai tambayoyin ya tambayi tsohon gwamnan Legas dalilin da yasa ya kasa bayyana ma ‘yan Najeriya tushen arzikin shi, kasancewar shi attajiri ne wanda rahotanni da dama suka yi zargin cewa ya kai biliyoyin naira, kuma yayi la’akari da irin gidan da ya ke da shi yana zaune a Legas.

Tinubu, wanda da alama bai ji dadin wannan tambayar ba, ya tambayi mai tambayoyin yadda ya san cewa yana da arziki tun da shi ba akawun shi ba ne. Duk da haka, ya kuma bayyana cewa mai tambayoyin ya kamata ya san yadda ake yin tambayoyi ba tare da zargin shi ba.

Advertisement

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya kuma tambayi mai yi mai tambayoyin ko su makiyan arziki ne, idan kuma ba makiyan arziki ba ne, ya kamata su fahimci cewa jarin yana samun albarka, kuma kamar yadda Warren Buffet, wanda ya kasance daya daga cikin attajirai a Amurka da kuma masu kudi duniya, ya samu kudin shi daga siyan haja, shi da kan shi ya gaji dukiya mai yawa ya juya darajar ta.

Tinubu yayi nuni da cewa ba wai yana karyata dukiyar shi ba ne, kuma a matsayin shi na dan takarar da aka fi bincike tun bayan da ya bar mulki a matsayin gwamnan jihar Legas, bai samu wani nadin gwamnati ko kwangila ba, kuma kungiyoyi da dama sun wanke sunan shi.

Advertisement