Al'umma

Amotekun: Matasan Arewa sun gargadi Gwamnan Ondo kan cin zarafin yan Arewa

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewacin Najeriya (AYCF) a ranar Juma’a, ta gargadi gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, inda ƙungiyar tayi kira gare shi da ya kawo karshen cin zarafin yan Arewa da jami’an tsaro na yan bangar (Amotekun) ke yi a jihar.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Yerima Shettima ya sanyawa hannu, ta yi zargin cewa a lokuta da dama, jami’an rundunar Amotekun na karbar yan Arewa da kuma cin zarafin yan Arewa a jihar ba tare da wani dalili ba.

Sanarwar ta ce kasancewar jami’an SSS, Sojoji, Amotekun, NSCDC da sauran jami’an tsaro an samar da sune don kare rayuka da dukiyoyi ba don muzgunawa mazauna garin ba.

Advertisement

Ya kara da cewa bai kamata a rika amfani da Amotekun Corps mallakin gwamnati ba a kan wasu tsirarun yan Arewa mazauna jihar ba, wadanda kawai suke gudanar da sana’o’in su na halal.

Sanarwar ta sanar da gwamnan cewa, kasancewar yan Arewa suna jihar ne don gudanar da sana’o’in su na halal, haka ma akwai yan kudancin kasar da suka bazu a sassan Arewacin kasar nan.

Shettima ya kara da cewa, idan aka cigaba da yi musu irin wannan muzgunawa, tsana da tsangwama, ba za’a samu zaman lafiya a kasar nan ba.

Kungiyar ta yi gargadin cewa, idan har gwamnatin jihar Ondo ta bar irin wannan tursasa da cin zarafi, ba tare da hujja ba, hakan na nufin baya son yan Arewa a jiharsa.

Advertisement