Amfanin Gwaiba Ga Lafiyar Jiki
Gwaiba (Guava) maganin gargajiya ce wacce ke maganin cututtuka da dama. Bincike na farko ya nuna cewa sinadaran dake cikin ganyen gwaiba na iya yin tasiri a kan nau’o’in cututtuka masu yawa, ciki har da ciwon wanda ya shafi matsalolin haila a bangaren mata, gudawa, mura, nau’in ciwon sukari na 2 (diabetes), da ciwon daji (Cancer).
Ganyen gwaiba yana sinadarai masu yin magani. Idan aka tsatsi ruwan ‘ya’yan itacen na gwaiba aka sha a baki sana ba da taimako daga sanyi da tari ta hanyar rage daskararar majina a maƙogwaro, da kashe ƙwayoyin cuta da kuma hana ƙwayoyin cuta a cikin makogwaro saboda yanayin astringent, wanda shima wani sinadari mai muhimmanci.
Ko da yake an san gwaiba tana amfani daban-daban, wani bincike na baya-bayan nan ya nuna wani fa’ida game da ganyen gwaiba a cikin maganin wanke baki domin yana taimakawa wajen rage ciwon aphthous (cututtuka a baki).
Domin samun ƙarin wasu fa’idodi na gwaiba sai ku cigaba da bin akan wannan shafin yanar gizo na Arewa Times Hausa, ko kuma a tuntuɓe mu kai tsaye ta wannan adireshin Email:- info@arewatimes.com.ng