Tsaro

Alkawarin da Osinbajo ya yiwa tubabbun ƴan Boko Haram a Borno

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yiwa yan Boko Haram da suka tuba alkawarin cewa gwamnatin tarayya zata tallafa musu da hanyoyin samun kudin shiga.

Osinbajo yace halastattun hanyoyin samun kudin shiga zai taimaka musu su fara sabuwar rayuwa.

Ya yi magana ne a sansanin Hajji da ke Maiduguri, a ranar Alhamis, a ziyarar aiki da ya kai jihar domin kaddamar da asibitin MSME da kuma kaddamar da ayyuka daban-daban da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar.

Advertisement

Osinbajo ya kuma yi wa ’yan ta’addan da suka tuba alkawarin cewa gwamnati za ta samar musu wurin zama, aiki, da gudanar da sana’arsu ta halal.

Ya kuma ba su tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta kula da su ta hanyar da ta dace.

A cewar Osinbajo: “Ni ne shugaban kwamitin shugaban kasa kuma mai girma Gwamna Zulum shine mataimakin shugaban kwamitin.

Advertisement