Al'umma

“Aji tsoron Allah, Jesus yayi kusan dawowa” – Inji wani Fasto a Masallacin Juma’a

Fasto ya zo kusa da Masallacin Juma’a yana cewa aji tsoron Allah Jesus ya kusa zuwa

Wani Malamin Addinin Kirista ya zo kusa da Babban Masallacin Juma’a na babbar kasuwar kayan abinci a Legos-stred da ke birnin Benin jihar Edo, yana yiwa Musulmai da kirista wa’azin cewa su ji tsoron Allah Jesus ya kusa bayyana.

Wannan ya faru ne a yau Juma’a, ana gab da fara huɗubar Juma’a a babban Masallacin Juma’a na kasuwar.

Advertisement

Inda yazo ɗauke da Littafinsa na Bible yana cewa “Aji tsoron Allah, Masu sata su daina, masu zinace-zinace su daina, masu garkuwa da mutane su bari, su tuba su ji tsoron Allah, saboda Jesus ya kusa zuwa” Cewar Faston.

Ya Kara da cewa masu shan giya da masu Kidnapping su tuba su daina, Isa ya kusa bayyana, Duniya ta kusa tashi.

Mene ne ra’ayoyinku game da wannan?

  • Daga: Usman Umar Katsina

Advertisement