Al'umma

Aisha Buhari ta mayar da martani bayan kai wa Amaechi da matar shi ziyarar taya murna (Hotuna)

Aisha Buhari, wadda ita ce uwargidan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ta raba kayatattun hotuna da ta dauka a lokacin da ta ziyarci tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan sufuri na kasar, Rotimi Amaechi.

Aisha Buhari ta raba kayatattun hotunan a shafinta na Facebook da aka tabbatar a yau.

Ta ce ta samu tarba ne daga mai girma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da matar sa, Dame Judith Amaechi a lokacin da ta kai musu ziyarar taya murna.

Advertisement

Ku tuna cewa majalisar masarautar Daura ta jihar Katsina ta ba tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress mukamin sarautar Dan Amana na Daura a kwanakin baya.

Mijin Aisha, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ne daga garin Daura da ke jihar Katsina a yankin Arewacin Najeriya.

Wannan rubutu da Aisha Buhari ta yi a baya-bayan nan ya haifar da so da tsokaci daga masoyanta da dimbin mabiya a dandalin sada zumunta.

( Source News – Aisha Muhammadu Buhari Verified Facebook Page )

Advertisement