Al'umma

Aisha Buhari ta kai wa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ziyara [Hoto]

Uwargidan Shugaban Tarayyar Najeriya, Dakta Aisha Buhari ta kai wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ziyara.

A cewar wani rahoto, Mista Yari ya dade yana fama da ciwon gwiwa.

A jawabin da ta yi tun farko a yau, Aisha ta yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya cikin gaggawa, sannan ta kuma yi masa fatan samun nasara a ayyukan sa na gaba.

Advertisement

Uwargidan shugaban kasa ta samu rakiyar mataimakiyarta Hajiya maryam.

A nasa jawabin, Yari ya gode mata da irin wannan karamcin da ta yi mata tare da yi mata addu’a Allah ya saka mata da alheri.

An dauki hoton wannan group ne a lokacin da uwargidan shugaban kasar ta iso tare da tawagarta a gidan AA yari

Advertisement