Ra'ayoyi

Aikin Ƴan Sakai: Fa’idodi, Haɗari Da Ƙalubale

Harbin bindiga a cikin dare na zama abin dawwama a yankunan karkara da kewaye a wasu sassan Najeriya. Hatta sautin faɗuwar abu da ya faɗo ƙasa za’a iya ɗaukar cewa harbin bindiga ne daga ƴan bindiga, ƴan ta’adda ko masu garkuwa da mutane da ke shirin tayar da tarzoma, ko kuma farar hula da ke ƙoƙarin kare al’ummarsu.

Wani lokaci, harbi na iya nuna cewa farar hula dake banga sun yi kiciɓis yan ta’adda/masu garkuwa da mutane dake tunkarar al’ummarsu.

Harbin bindigar na iya korar yan ta’adda/ masu garkuwa da mutane. Yana tsoratar da yan ta’adda / masu garkuwa da mutanen da jama’ar gari ke gadi, suna tsare kansu da iyalansu da dukiyoyinsu. Galibi, ƴan ta’addan/masu garkuwa da mutane suna ƙaura zuwa yankunan dake makwabtaka da su don neman waɗanda za su iya kamawa, ba tare da saninsu ba, yayin da suke barci ba tare da tsaro ba.

Wannan tsarin na farar hula na banga na samar da wani nau’i na walwala a yawancin al’ummar kasar nan, musamman a Arewacin Najeriya. A al’ada, wannan ya haifar da yaduwar ƙananan ƙungiyoyin farar hula masu zaman kansu a cikin al’ummomin da ke bayan gari, kewayen birni da yankunan karkara.

Za a iya gano nau’o’in farar hula guda biyu na aikin banga ko sintiri a duk faɗin ƙasar. Na farko, ƙungiyoyin farar hula da suka shirya waɗanda ke da jagoranci kuma suna ɗaukar sunayen mabambanta, kamar Civilian Joint Task Force, Vigilante Group of Nigeria, ‘Yanbanga’, ‘Yansakai’ da wasu sunaye da dama da aka zaɓa bisa yare na cikin gida.

Ƙungiya ta biyu ta ƙunshi ɗaiɗaikun farar hula, yin ƙoƙari don kare iyalansu kuma a wasu lokuta, na iya yin aiki tare da yan sanda a cikin al’umma. Ba tare da la’akari da nau’in ba, aikin banga na farar hula a yankunan karkara yana da matukar wahala kuma yana da barazana ga rayuwa, saboda yankunan karkara sun fi fallasa kuma suna da karancin tsaro.

Nasarar da farar hula ke samu na aikin “Sa Kai” yayi yawa a wasu sassan kasar. A shekarar 2021, wani harin kwantan bauna da wasu yan banga suka yi a wata jiha a yankin Arewa maso Yamma, yayi sanadin kashe yan ta’adda da dama. An yi imanin cewa ‘yan ta’addar suna tsoron wasu al’ummomi kamar gobarar daji, saboda tsananin tsarinsu na banga. To sai dai kuma idan tawagar yan bangar da kanta ta yi rashin sa’a ko kuma yan ta’addan suka haɗu tawagar da ba su da horo da kuma rashin isassun kayan aiki, jaridun Najeriya za su cika da rahotanni asarar rayuka, raunuka da kuma yawan mutanen da aka sace.

A wasu lokuta na nadama, yan ta’adda suna jiran lokacin mafi rauni, lokacin da tsarin aikin yan banga ya sassauta. Wani abin da aka fi sani da shi ne, da zarar karfe 2:00 na dare yayi hankali ya tashi domin yan ta’addan kan kai hari a wasu lokuta a wannan lokacin, don ba su damar yin tafiya mai nisa da kai wadanda abin ya shafa a maboya, inda masu wucewa ba sa iya gane su, kauyuka ko gonaki.

A watan Janairun 2022, mazauna wasu kauyukan jihar Zamfara sun yi zargin cewa wasu yan bindiga sun kashe mutane kusan 200, ciki har da yan banga a wani hari guda. Lokacin da yan ta’adda suka mamaye al’ummomi, ƙoƙari na farko shine kawar da duk wani mutum da ke da hannu a aikin yan banga don su ne babbar barazana gare su.

Wadannan kungiyoyin farar hula masu dauke da makamai masu zaman kansu basu samun komai daga gwamnatin karamar hukuma ko jiha a Arewacin Najeriya. A kusan dukkan jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro a arewacin kasar, akwai kungiyoyin farar hula masu ƙoƙari, masu rike da makamai, suna aikin banga a yankunansu. A wasu al’ummomi, yan kungiyar sun sami ilimi mai mahimmanci akan laifuka, makamai da kuma amfani da makamai. Idan aka kyale su, za su iya haifar da babbar barazana ta tsaro a nan gaba, musamman ganin yadda ake samun yawaitar makamai da kananan makamai a kasar.

Kwarewar ƙungiyar ƴan banga ta al’umma, wacce ta juya yan fashin birni, Bakassi Boys, har yanzu tana cikin abubuwan tunawa.

Back to top button