Al'umma

Afrika: Yan ci-rani 6 sun mutu, 30 sun bace, bayan kwale-kwalen su ya nutse a gabar tekun Tunisiya

An tabbatar da mutuwar wasu bakin haure 6 yan Afirka da suke kokarin tafiya Turai, sannan an bayyana bacewar wasu mutane 30 a tekun Mediterrenean bayan kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar tekun Tunisiya a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Tunisia ta fitar a ranar Juma’a, sojojin ruwa da na bakin teku na arewacin Afirka sun kwaso gawarwakin, sannan an ceto mutane 34 da suka tsira tare da cigaba da neman mutanen da suka bace.

“Wadanda suka tsira sun shaidawa masu ceto cewa jirgin na da mutane 70 kuma sun nufi Italiya,” in ji ma’aikatar.

Advertisement

“Jirgin ruwan ya taso ne daga makwabciyar kasar Libya kuma ya nutse a nisan kilomita 40 daga garin Zarzis na kasar Tunisiya, kusa da kan iyakar kasar Libya.

“Wadanda suka tsira sun hada da mutanen Masar, Sudan da Ivory Coast,” in ji Mongi Slim, shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Tunisiya.

Ma’aikatar tsaron Tunusiya ta ce hukumomi sun dakile balaguron balaguron kwale-kwale guda takwas a cikin sa’o’i 48 da suka wuce a gabar tekun birnin Sfax, kuma an tsare mutane 130 daga Tunisiya da yankin kudu da hamadar Sahara.

Advertisement