Wasanni

AFCON 2021: Senegal ta lallasa Masar domin lashe kofi

Kungiyar Teranga Lions ta doke Masar da ci 4-2 a bugun fanariti a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2021 a daren Lahadi, inda suka dauke kofin.

Advertisement

An buga wasan karshe na AFCON na 2021 a filin wasa na Paul Biya, Olembé, a Kamaru.

An tashi wasan ne ci 0-0 bayan da Senegal da Masar suka kasa cin kwallo bayan mintuna 120.

Advertisement

Sai dai Senegal ta lallasa Masar da bugun fanariti inda ta lashe gasar AFCON ta farko.

A baya Senegal ta sha kashi a wasannin karshe na AFCON biyu a baya, na baya-bayan nan na 2019, inda ta sha kashi a hannun Algeria a wasan karshe.

Advertisement