Wasanni

AFCON 2010: Yadda Mali ta ci ƙwallaye (4) cikin minti 11 a wasan da suka tashi 4-4 da Angola

Tawagar kwallon kafar Angola da Manuel Jose ya jagoranta sun fafata da tawagar kasar Mali karkashin jagorancin Stephen Keshi a gasar AFCON a shekarar 2010.

Angola ta tashi 4-0 a minti na 78 da fara wasan inda Flavio ya zura kwallo biyu a raga yayin da Gilberto da Manucho suka ci kowanne.

Sai dai Keita ya zura kwallaye biyu a raga yayin da Kanoute da Yatabare suka ci wa Mali kowannen su, inda suka zura kwallaye hudu a cikin mintuna 11 da suka tashi 4-4.

Advertisement