Al'umma

Abin Yana Yi Min Zafi Idan Ana Cewa Fulani Yan Ta’adda Ne, Domin Ni Bafulatani Ne – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadin shi kan yadda ake ganin cewa duk Fulani ne masu laifi ne. Ku tuna cewa a jiya ne dan takarar PDP ya je jihar Oyo domin ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a wani bangare na yakin neman zabensa gabanin zaben 2023.

Yayin da yake gabatar da jawabin shi, Atiku ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa ya magance matsalolin tsaro da ke barazana ga kasar idan ya zama shugaban kasa. Ya ce ya kan yi masa zafi idan wani ya ce Fulani ne masu laifi domin shi Bafulatani ne.

A cewar Atiku, mutane ba su zama masu laifi saboda kabilar su ko addinin su domin akwai miyagun mutane a kowace kabila da addini.

Advertisement

“Mun kuma yi alkawarin dawo da tsaro a kasar nan, ba ka san yadda abin yake min zafi a zuciyata ba idan ka ce Fulani ne masu laifi, saboda ni bafulatani ne, don haka bari in gaya maka cewa za mu yi maganin masu aikata laifuka a kowane bangare na kasar nan da suka fito.” Ya kara da cewa.

Advertisement