Siyasa

Abin da yasa sabuwar jam’iyyar Kwankwaso ba zata iya ci zaben 2023 kamar yadda APC ta yi a 2015

Kwanan nan, Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, da wasu mutane sun hada karfi da karfe a karkashin (The National Movement) da nufin samar da sabuwar jam’iyya.

Yayin da wasu ke kwatanta bullowar sabuwar jam’iyyar da za su da za’a kafa nan ba da dadewa ba da fitowar jam’iyyar All Progressives Congress APC, kafin zaɓen 2015, akwai alamar tambaya ko rundunar wankwaso zata iya samun nasara a matakin shugaban kasa.

Mutanen da ke da niyyar kafa jam’iyyar, wadda ta sha bamban da yadda jam’iyyar All Progressives Congress APC ta kafu a lokacin da irin su Bola Ahmed Tinubu, Shugaba Muhammadu Buhari, Cif Bisi Akande, da dai sauransu suka kafa ta.

Advertisement

Ta fuskar mutanen da suka kafa APC, za’a iya cewa sun yi kasuwanci ne kuma a shirye suke su baiwa jam’iyya mai mulki ta PDP fafatawa mai tsanani a matakin kasa baki daya.

Kamar yadda aka bayyana a baya, APC ta kunshi ’yan siyasa irin su Tinubu, Shugaba Buhari, Adams Oshiomole, da wasu manyan ’yan siyasa irins u Rotimi Amaechi, Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso da kan sa, daga baya ya koma jam’iyyar.

Idan aka yi la’akari da mutanen da suka kasance a jam’iyyar APC a lokacin, za’a ga cewa kowane yanki na kasar nan yana da wakilci a jam’iyyar da yan siyasar da za su iya yin tasiri a harkokin siyasa a yankunan su.

To sai dai idan aka yi la’akari da jam’iyyar Kwankwaso da sauran su ke kafawa, za’a iya cewa duk da cewa ‘ya’yan kungiyar manyan ’yan siyasa ne, amma ba zasu samu irin tasirin siyasar da suke da shi ba wajen cin zabe na kasa kamar zaben shugaban kasa.

Baya ga wasu yan kungiyar, wasu ba za su iya daukaka farin jinin da wadanda suka kafa jam’iyyar APC irin su Bola Tinubu, Shugaba Muhammadu, da sauran su zasu iya bunkasa ta a lokacin da suka fara jam’iyyar All Progressive Congress APC ba.

Advertisement