Siyasa

Abin da na fadawa Buhari game da takarar shugaban kasa ta 2023 – Tinubu

Babban jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu, yace a ranar Asabar din da ta gabata ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yana son ya gaje shi a matsayin shugaban kasa ba wai ya taka kafar shi ba.

Tinubu  ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja, a watan Janairu, inda ya sanar da shi aniyar shi ta tsayawa takarar kujerar mafi girma a siyasar kasar nan a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Alake na Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo, a Abeokuta, jihar Ogun.

Advertisement

Yace: “Na gayawa Shugaban kasa ina so in maye gurbin shi kuma ba na son in bata mai rai. Na gayawa Shugaban kasa cewa ina so in taka sawu amma ba taka kafar shi ba.

“Nace masa a matsayi na na daya daga cikin yan kasa, ya kamata in fara takarar shugaban kasa ta hanyar sanar da kai tukuna, shi kuma (Buhari) yace in sanar da duniya baki daya, kuma na yi hakan.”

Advertisement