Siyasa

Abin Da George Bush Yayi Da Na Sanar Shi Obasanjo Na Son Yin Wa’adin Mulki Na 3 – Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya mayar da martani kan kalaman da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi inda ya ce zai iya sake tsayawa takara karo na uku idan ya so kafin ya bar mulki a shekarar 2007.

Advertisement

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na TVC, Orji Kalu ya ce Obasanjo bai “fadi gaskiya ba a lokacin da ya ce idan yana son wa’adi na uku zai iya samu”.

A cewar Kalu, ya kasance kusa da Obasanjo, kuma ya yi kokarin shawo kan shi ya goyi bayan burin shi na neman wa’adi na uku a mulkin Najeriya. Ya ce a lokacin da ya gano cewa Obasanjo na shirin samun wa’adi na uku, sai ya sanar da George Bush wanda shi ne shugaban kasar Amurka a lokacin kuma ya gayyaci Obasanjo fadar White House.

Advertisement

A cewar Kalu, George Bush ya shaida wa Obasanjo a fadar White House cewa idan har yana son ya mayar da ‘yar shi ko mataimaki ahi ya zama shugaban kasa bayan kammala wa’adin shi na biyu yana da ‘yancin yin hakan amma ba za a bar shi ya yi na uku ba.

Da yake karin haske, Kalu ya ce shugabannin wasu kasashen Afirka su ma sun hada hannu wajen karya ajandar Obasanjo na wa’adi na uku.

A ainihin kalmomin Kalu: “…A’a bai iya yin hakan ba, mun fi shi karfi da yin hakan. Mun jira shi, duk duniya ba Afirka kadai ba saboda yana so ya fara zango na uku ta hanyar samun shi. wa’adi na uku a AU (Tarayyar Afirka) lokacin yana shugaban kungiyar AU kuma wannan ne ya sa wasu abokan aikin shi a Ghana, Afirka ta Kudu, da wata kasa suka je suka kawo shugaban Tanzaniya ya zama shugaban AU, wato, farkon. Kuma na gaya wa Shugaba George Bush cewa yana son yin wa’adi na uku kuma suna jiran shi, George Bush ya gaya masa cewa zai iya sanya ‘yar shi, zai iya sanya mataimakin shi amma ba kan shi ba. Ba zai iya fitowa ya gaya wa ‘yan Nijeriya cewa ba ya son yin wa’adi na uku ba”.

Advertisement