Abinda Baku Sani Ba Game Da Sakin Aure A Turai, Amurka Da Najeriya

Assalamu alaikum warahatullahi ta’ala wabarakatuhu. Jama’a masu karatu barka da wannan lokaci, da fatan kuna lafiya.

A yau zamu yi zuwa ga sake-saken aure a ƙasar Amurka da Najeriya mu mene ne bambanci a kasashen biyu.

Sakin aure a Amurka ba kamar yadda wasu mutane ke tunani ba ne, eh gaskiya ne ana sake-saken aure a kasashen Turai (Europe), ciki har da Amurka.

Sai dai sakin aure a Amurka ko Europe yana da wahalar gaske fiye da yadda kuke zato.

Ga waɗannan su bayanai da kuke bukatar sani game da sakin aure a Amurka ko Europe (Turai);

Kuɗin yarjejeniya: Yawanci akwai kuɗin yarjejeniyar aure da miji da mata za su rattaba akai kafin a kai auren. Idan ɗaya daga cikin ma’auratan ya nemi saki bayan auren, zai biya ɗayan waɗannan kuɗaɗen.

Hasali ma, kuɗaɗen sukan kai maƙuden miliyoyin dalolin Amurka! Misali, kuɗin da Jeff Bezos (Mai kamfanin Amazon) ya biya matar shi da ya saka, an hasashen cews sun fi yawan kuɗin attajirin nan Alhaji Aliko Ɗangote ya mallaka.

Mazauni bayan saki: A Europe, ba zaka saki mace ba ka tafiyar ka ba, ka bar ta da wahalar biyan kuɗin gidan haya da yara da kuma sauran abubuwa na yau da kullum.

Kun san kuma haya na tsada a Europe da Amurka, kuma duk wata ake biya. Ko kwanan nan sai da wata kotu ta tilastawa wani ɗan ƙasar Ghana (Da ya auri Baturiya) barin gidan shi. Kuma zai cigaba da biyan rabin kuɗin haya da sauran hidimar gidan, duk cewa da ba ya zama cikin gidan.

Saboda dalilan muka ambata a sama guda biyu, mutane da yawa suna gudun aure a Europe da Amurka.

Yana daga cikin irin wadannan dalilan, wasu sun gwammace zama a tare da mace har su hayayyafa ba tare da sunyi aure ba. Misali, Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez har yanzu ba su yi aure ba tun 2017, amma sun haihu.

Yara a Europe wani lokaci sukan faɗawa cewa iyayen su ba su taɓa aure ba. Wasu kuma sukan ce ba za su yi aure ba. Duk da dai wasu da nasu dalilan, amma yawanci saboda tsoron wahalar rabuwa.

Ya kamata ku san cewa yana za’a iya ɗaukar shekera guda ana zuwa wajen hukuma ana cike-ciken takardu.