Tsaro

Abin da ƴan Boko Haram suka gaya mini lokacin da na hadu da su – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu daga cikin tattaunawar da yayi da wasu yan kungiyar Boko Haram da ya hadu da su a shekarar 2011, yace baya ga masu sha’awar Shari’a, kungiyar ta koka da cewa mabiyan su ba su da wani aikin yi.

Obasanjo ya gana da yan kungiyar da kuma wasu iyalan Mohammed Yusuf, wanda ya kafa kungiyar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa taron na 2011 da aka yi a dangin Yusuf a Railway Quarters, hedkwatar kungiyar da aka rusa, ya dauki kusan mintuna 90.

Advertisement

Obasanjo ya bukaci yan Boko Haram su yi hakuri su manta da abin da ya faru a baya. An ruwaito a wurin taron cewa:

“Wannan shiri ne na sirri. Ina rokon ka da ka yafe ka manta da abin da ya gabata. Ina rokon ku, ku ba ni dama in shiga tsakanin ku da gwamnati.”

Da yake mayar da martani ga tsohon shugaban kasar, Babakura Fugu, surukin Yusuf, wanda aka kashe mahaifin shi a shekarar 2009, yace:

“Tun daga 2009, wannan shine karo na farko da wani babban jigo zai jajantawa dangin.

“Mun yi farin ciki da wannan ziyarar. Kusan kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na mambobin mu suna warwatse a kasashe makwabta na Chadi, Nijar da Kamaru.”

Tsohon shugaban kasar yace rashin tafiyar lamarin yadda ya dace da gwamnati ta yi shi rikicin ya wuce wuri.

Obasanjo ya kuma dora alhakin rashin tsaro a kasar kan samun makamai bayan yakin basasar Najeriya.

Yace: “A shekarar 2011, lokacin da Boko Haram ke kara girma, sai na je Maiduguri domin in yi bincike kadan game da Boko Haram da kuma gano mene ne manufar su baya ga sha’awar Shari’a, su ma sun yi korafin cewa mabiyan su ba su da wani aiki, kuma a kokarin su na samun wani abu da ya dace da kokarin taimakawa mambobin su.

A halin da ake ciki kuma, a yayin da yan ta’addan Boko Haram ke jibge makamai masu yawa, in Allah ya yarda za’a kawo karshen ta’addanci nan da shekarar 2023, a cewar Farfesa Babagana Zulum.

Vanguard ta rahoto cewa gwamnan jihar Borno ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, bayan ganawar shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Gwamna Zulum ya shaidawa manema labarai na fadar gwamnatin jihar cewa yana da yakinin cewa kalubalen da masu tayar da kayar baya ke haifarwa zai kawo karshe a cikin wa’adin mulkin sa wanda zai kare a shekara mai zuwa.

Channels TV ta kara da cewa a ganawar shi da shugaban na Najeriya, Zulum yace ya je fadar shugaban kasa ne domin sanar da Buhari irin ci gaban da aka samu wajen mika wuya na yan ta’addar Boko Haram.

Advertisement