Tsaro

Abdulmalik Tanko ya musanta garkuwa da Hanifa da kashe ta

Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar da ya amsa laifin sace dalibar shi Hanifa Abubakar mai shekaru 5 tare da kashe ta a kwanakin baya, a yau ya musanta tuhumar da ake masa ta kisan kai.

Advertisement

An ta habarto cewa, gwamnatin jihar Kano ta shigar da tuhume-tuhume biyar a kan Mallam Tanko, tare da wasu abokan shi biyu, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, a gaban wata babbar kotu ta 5 a jihar.

An tuhumi mutanen uku da laifin hada baki, garkuwa da mutane, boyewa da tsare wacce aka yi garkuwa da ita da kuma kisa, laifin da ya sabawa sashe na 97, 274, 277 da 221 na kundin laifuffuka.

Advertisement

Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen a ranar litinin, sun ki amsa dukkan laifukan da ake tuhumar su da su.

Advertisement