Al'umma

Abba Kyari yayi karar gwamnatin Najeriya akan cigaba da tsare shi da NDLEA ta yi

Dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda (DCP) Abba Kyari dake tsare a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ya shigar da karar a gaban kotu a kokarin shi na ganin an dawo masa da yancin shi na dan adam kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Advertisement

An kama Kyari ne aka mika shi ga hukumar NDLEA dangane da cinikin miyagun kwayoyi, kuma ya shafe kusan kwanaki uku a hannun hukumar.

Sai dai ya garzaya babban kotun tarayya dake Abuja a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, inda ya bukaci kotun ta ba da umarnin a sake shi ko kuma a ba shi beli.

Advertisement

Advertisement