Tsaro

Abba Kyari ya rude bayan wadanda ake zargi tare da shi sun amsa laifin fataucin muggan kwayoyi

Wani karamin wasan kwaikwayo ya faru a wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke da zaman ta a Abuja a ranar Litinin din nan, bayan da wasu da ake tuhuma tare da mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari, suka amsa laifin da ake zargin su da shi na safarar miyagun kwayoyi.

Advertisement

Sai dai duk da laifin da suka amsa, kotu tayi umarnin da a cigaba da tsare su a hannun hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) har zuwa ranar litinin ta mako mai zuwa inda za a saurari bukatar neman belin su.

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NDLEA ta gurfanar da Abba Kyari da jami’an ‘yan sanda shida da wasu fararen hula biyu a gaban kuliya bisa tuhumar su da laifuka takwas da suka hada da hada baki, hana ruwa gudu da mu’amala da hodar iblis da sauran laifuka.

Advertisement

Yayin da Kyari da wasu mutane uku da ake kara, wadanda ‘yan sanda ne suka ki amsa laifukan guda takwas da ake tuhumar su da su, fararen hula biyu, Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, sun amsa laifuka na 5, 6 da 7, inda sunayensu ya bayyana.

Advertisement