Al'umma

Abba Kyari ya nemi NDLEA ta ba shi diyyar miliyan ₦500 kan tsare shi ba bisa ka’ida ba

DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar a makwannin baya, ya bukaci hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta biya shi diyyar Naira miliyan ₦500 bisa zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Kyari, a cikin wata bukata ta asali mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, wanda aka shigar a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya kuma bukaci a ba hukumar NDLEA umurnin ta mika masa takardar ban hakuri a rubuce da jaridun kasar guda biyu.

Bukatar, mai kwanan wata 16 ga watan Fabrairu, kuma lauyansa, CO Ikena, ya shigar a ranar 17 ga watan Fabrairu, ta kuma bukaci a ba da umarnin “hana wanda ake kara (NDLEA), jami’anta, bayinsa, ’yan sanda, masu zaman kansu ko kuma duk wanda ke wakiltar su daga ci gaba da cin zarafi, tsarewa, tsoratarwa, kama mai nema ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

Umarnin da wannan kotu ta bayar na umurtar wanda ake kara da ya biya N500,000,000.00 (Naira miliyan dari biyar) ga wanda ake kara, saboda tauye hakki da kundin tsarin mulki ya tanada a sashe na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya. (Kamar yadda aka gyara)

Advertisement