Tsaro

Abba Kyari na iya kara kwanaki a tsare, yayin da NDLEA ta dauki muhimmin mataki

Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da wasu mutane hudu na iya kara zama a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya dake Abuja inda ta sanar da kotun aniyar ta na tsare wadanda ake zargin sama da awanni 48 da aka kayyade.

Da yake zantawa da wata majiya mai tushe a hukumar, The Punch ta bayyana cewa Abba Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga ci gaba da bincike don haka hukumar NDLEA ba za ta iya gurfanar da shi a gaban kuliya ba.

Advertisement

An kuma bayyana cewa tuni hukumar ta NDLEA ta fara gudanar da bincike kan hodar iblis da babban jami’in ‘yan sandan ya kama.

Majiyar ta ce: “Abba Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga karin bincike.

Har ila yau, hukumar ta NDLEA na gudanar da binciken kwakwaf kan wasu hodar iblis da Kyari ya kwato tun bayan da ya yi ikirarin cewa a cikin wani faifan bidiyo ya maye gurbin hodar iblis din da tabar wiwi.

“Don haka hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda muka sanar da kotu aniyar mu na kara yi masa tambayoyi da kuma tabbatar da wasu daga cikin abubuwan da ya ce ya yi.”

Kazalika, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta bayyana cewa ba ta da wani dalili da za ta kare duk wanda za a tuhume shi a ci gaba da gudanar da bincike kan wata badakalar safarar miyagun kwayoyi mai nauyin kilogiram 25 da ta hada da wata kungiya karkashin jagorancin DCP Abba Kyari.

Hukumar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu, ta ce ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da bincike kan hujjoji kuma ba za ta iya raunana kudurin ta ba ta hanyar bata gaskiya, inji rahoton The Nation.

Jaridar The Punch ta kara da cewa, martanin hukumar ta NDLEA ya biyo bayan rade-radin da ake yi na cewa za ta yi kokarin kare jami’anta da ke da hannu a lamarin.

A halin da ake ciki, babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami (SAN), ya ce gwamnatin tarayya da gwamnatin Amurka suna tattaunawa kan yiwuwar mika Kyari.

Malami ya yi magana ne a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, yayin da ya bayyana a matsayin bako a shirin ‘Siyasar Yau’ na Channels Television.

AGF ta kuma ce an kafa dalilai masu ma’ana na zargin Kyari.

A baya dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dakatar da Kyari bisa zarginsa da hannu a badakalar dala miliyan 1 da Ramon Abbas, wanda ake kira Hushpuppi ya shirya.

Advertisement