Al'umma

A kwai buƙatar a samar da hanyoyin rage yawan haihuwa cikin sauri – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira da a samar da ingantaccen tsarin kula da karuwar al’ummar kasar ta hanyar ingantaccen tsarin kula da lafiya.

Buhari yayi wannan kiran ne a ranar Alhamis, a wajen kaddamar da sabon tsarin manufofin jama’a don cigaba mai dorewa a fadar gwamnati dake Abuja a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar.

A cewar shugaban, manufar shirin ita ce tabbatar da samun koshin lafiya ta hanyar bullo da shirye-shirye da nufin gyara yawan haihuwa.

“Manufar ta jaddada gaggawar magance matsalar yawan haihuwa a Najeriya, ta hanyar fadada hanyoyin samar da tsarin iyali na zamani, shawarwari da kayayyaki tare da inganta tazarar haihuwa.

“Hakan zai baiwa Najeriya damar samun nasarar hana haihuwa cikin gaggawa, da inganta lafiyar mata, matasa, jarirai da yara, da sauran kungiyoyin al’umma.

“Sauran mahimman bayanai na manufofin yawan jama’a da aka sake fasalin sun nuna mahimmancin saka hannun jari don ingantaccen ilimin matasa (musamman mata), haɓaka jarin ɗan adam, haɓaka cikakken ƙoƙarin cimma gagarumin sauyin alƙaluma.

Manufofin yawan jama’a da aka sake fasalin na da wadata da duk wasu muhimman bayanai da za su jagoranci aiwatar da Tsare-tsare na Tsakanin Wa’adi da Ra’ayin Ci Gaban Nijeriya.

Shugaban ya kara da cewa, “Zai kara magance matsalolin dimbin matasa wadanda su ne abin alfaharinmu, makomarmu da dukiyoyinmu don ciyar da kokarinmu na ci gaban kasa.”

Advertisement