Labarai

A Cikin Ƙasa Da Watanni 6 Isra’ila Ta Wargaza Gaza

Kamar yadda muka bayyana a baya, Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ya fitar da wani rahoto da ke cewa akwai “dalilai masu ma’ana” da ake ganin Isra’ila na aikata kisan kiyashi a zirin Gaza.

Da yake gabatar da binciken a Geneva, Albanese ya ce an yi amfani da tan 25,000 na bama-bamai – kwatankwacin bama-baman nukiliya guda biyu, an yi amfani da su wajen wargaza yankunan Gaza gaba daya, “suna shafewa ko lalata kusan dukkanin kayayyakin more rayuwa.

Haka zalika, filayen noma, galibin gidaje, wuraren kiwon lafiya, hanyoyin sadarwa, kowace jami’a, mafi yawan wuraren ilimi da wuraren tarihi na al’adu marasa adadi duk Isra’ila ta wargaza su da bama-bamai”.