Siyasa

2023: Zan yi takara ne domin in kyautata makomar ƴa’ƴan mu – Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Najeriya na bukatar shugaban da ya cancanta da zai hada kan al’umma da magance matsalar rashin tsaro da farfado da tabarbarewar tattalin arziki da kuma amfanar da talakawa a wannan karon.

Tinubu, wanda ya je jihar Ekiti a cigaba da tuntubar juna kan zaben shugaban kasa a 2023, ya ce ya yanke shawarar tuntubar sarakunan gargajiya kafin ya bayyana hakan ne saboda irin muhimmancin da ya bai wa al’adu..

Yace, “Ina yin takara ne domin sabunta bege da kuma kyautata makomar yaran mu. Domin Nijeriya ta tsaya tsayin daka, ta cigaba, muna bukatar hakuri da hikima. Dole ne mu kasance da haɗin kai, ta haka ne kaɗai za mu iya zama babba.”

Advertisement

Tinubu, tare da rakiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Bisi Egbeyemi, wanda ya ce shi ya wakilci Gwamna Kayode Fayemi, da kuma jiga-jigan ajandar Kudu maso Yamma na Tinubu 2023, karkashin jagorancin Sanata Dayo Adeyeye, tun da farko sun gana da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Ekiti a wurin su. chambers a babban birnin kasar.

Advertisement