Siyasa

2023: Zan Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Idan….. – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana a ranar Litinin cewa zai janye daga takarar shugaban kasa a 2023 idan har aka samu abokin takarar shi, Datti Baba-Ahmed, yana cin hanci da rashawa.

Obi, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi a gidan Chatham da ke Landan, ya ce Baba-Ahmed bai taba yin kasa a gwiwa ba a lokacin da yake dan majalisar wakilai ta kasa ba.

Ya ce: “Za mu yaki cin hanci da rashawa, Datti yana da tarihin kasancewa dan majalisar kasa daya tilo da ya ki sayen kadarorin gwamnati a lokacin da aka yi tayin ga dukkan mambobin ta. Za ku iya zuwa ku duba tarihin shi, idan kun sami duk inda ya sanya kan shi a cikin ciniki cewa ya yi sulhu da matsayin shi, zan daina takarar.

Advertisement
Advertisement