Siyasa

2023: Yan Takarar 8 A PDP Sun Fice Daga Jam’iyyar Zuwa APC

Tsofaffin ‘yan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Zamfara 8 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Yusuf Idris ya fitar a Gusau, ta ce tsaffin ‘yan takarar sun bayyana sauya shekar su ne a wata ganawa da suka yi da Gwamna Bello Matawalle a jiya.

A cewar Idris, dukkan masu neman tsayawa takara sun halarci zabukan fidda gwani na jam’iyyar PDP a mazabunsu a fadin jihar.

Advertisement

Ya bayyana cewa wadanda suka sauya sheka sun hada da Kasimu Jafaru daga Zurmi ta Yamma, Rukkayya Abdullahi daga Zurmi ta Gabas, Isah Ibrahim-Labbo daga Anka, da Abubakar Abdulaziz daga mazabar Tsafe ta Gabas.

Karin mutanen da suka sauya sheka sun hada da Bala Ibrahim da Jamilu Bawa daga Birnin Magaji, Ibrahim Surajo daga yankin Zurmi ta Yamma, da kuma shugaban kungiyar Murtala Mainasara daga Shinkafi.

Advertisement