Siyasa

2023: Yahaya Bello zai bayyana takarar shi ta shugaban kasa bayan babban taron APC

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yace a ranar Laraba zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bayan babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya gudanarwa a wata mai zuwa.

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne jam’iyya mai mulki ta APC za ta gudanar da babban taronta na kasa.

Bello, wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da yan jarida a Lokoja, yan Najeriya na gida da waje sun yi ta matsa masa lamba kan ya tsaya takarar shugabancin kasar a wani yunkuri na kara karfafa nasarorin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu.

Advertisement

Yace: “Muna sa ran bayan babban taron jam’iyyar mu da yardar Allah zan bayyana. Amma dole ne mu sami hanyar da za mu yi aiki a kai kuma ita ce jam’iyyar All Progressives Congress. An gina jam’iyyar kwata-kwata a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni. Sun yi babban aiki, za mu kammala sauran a babban taronmu.

Bisa umarni da kiran yan Nijeriya, matasan Najeriya da mata da sauran jama’a a duk fadin duniya da suke kira na da in yi takara domin in cigaba da samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari. Tabbas zan amsa musu nan da nan bayan taronmu kamar yadda ya kasance.”

Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa APC za ta kara karfi bayan babban taron kasa.

Advertisement