Siyasa

2023: Tsofaffin Gwamnoni 2 a Kudu Maso Yamma, Da Ba Za Su Goyi Bayan Takarar Tinubu Ba

Alamu na nuna cewa wasu Tsofaffin Gwamnoni masu biyayya ga Tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba za su goyi bayan aniyar shi ta takarar shugaban kasa ba.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne Tinubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa ga jama’a, cewa zai tsaya takarar Shugaban kasa, a karkashin Jam’iyyar APC.

Tinubu ya bayyana haka ne ga jama’a a lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya sanar da shugaban burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.

Advertisement

Sai dai alamu sun nuna cewa wasu Tsofaffin Gwamnonin da Tinubu ya horas da su ba za su goyi bayan aniyarsa ta Shugaban kasa ba, saboda wani dalili.

Daya daga cikin Tsofaffin Gwamnonin da watakila ba za su goyi bayan Bukatar Shugabancin Tinubu ba, shi ne Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Akinwumi Ambode. Alamu sun nuna cewa watakila Ambode ba zai goyi bayan Bukatar Shugabancin Tinubu ba.

Dalili kuwa shine, ana rade-radin cewa Ambode zai iya tsayawa takarar Gwamna, a karkashin Jam’iyyar APC. A halin yanzu, gwamnan jihar, Babajide Sanwo-olu shi ma zai tsaya takara domin kammala zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Sai dai watakila Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai goyi bayan Bukatar Gwamna Ambode ba. Idan dai za a iya tunawa, an hana Ambode tikitin takarar Gwamna a karo na biyu, kuma an tattaro cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jagoranci yadda aka hana Ambode tikitin takarar Gwamna a karo na biyu.

Ko da yake, Ambode bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamna ba, amma alamu sun nuna cewa zai iya tsayawa takara a zaben fidda gwani da Sanwo-olu a Jam’iyyar. A halin yanzu dai, Tinubu ba zai sake mara masa baya ba.

Idan dai za a iya tunawa, Ambode bai taka rawar gani ba a Siyasar Jihar Legas, tun bayan da aka hana shi tikitin takarar Gwamna a karo na biyu a APC.

A kwanakin baya ne dai tsohon kakakin jam’iyyar PDP na jihar Legas, Ganiu Taofeek, ya yi kira ga Ambode da ya fice daga APC ya koma PDP. Hakan na nufin akwai wata alaka tsakanin Ambode da wasu Shugabannin PDP.

Wannan manuniya ce da ke nuni da cewa watakila Ambode ba zai rungumi burin takarar shugaban kasa na Tinubu a 2023 ba, idan har Ambode ya koma PDP. Ko da yake, Ambode ya zama Gwamna, tare da taimakon Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2015 amma ba zai goyi bayan burin sa na Shugaban kasa ba.

Wani tsohon Gwamnan da ba zai goyi bayan Bukatar Shugaban kasa na Tinubu a 2023 ba, shi ne tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola.

Alamu sun nuna cewa watakila Aregbesola ba zai goyi bayan Bukatar Shugabancin Tinubu ba, saboda rikicin da ke tsakaninsu. Idan dai za a iya tunawa, akwai rikici tsakanin Aregbesola da Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola, wanda Tinubu ya kasa sasantawa.

An tattaro daga Osun Defender cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar sun je Aregbesola, domin shiga rikicin da ke tsakanin Aregbesola da Gwamna Oyetola amma Tinubu ya ce musu ba zai iya shiga cikin rikicin ba.

An ruwaito cewa Tinubu ya yi alkawarin haduwa da ’yan uwa masu goyon bayan Aregbesola a jihar domin ya cuce su, kuma su marawa Gwamna Oyetola baya amma shugabannin sun yi watsi da kiran na Tinubu. Domin kuwa Tinubu ya ce ba zai iya kiran Aregbesola a tsari ba, hakan na nufin ba zai sake samun kyakkyawar alaka da shi ba, kuma ba zai goyi bayan aniyarsa ta Shugaban kasa ba.

Advertisement