Siyasa

2023: ‘Tinubu ya je ya huta, zan zabi Osinbajo’ – Edwin Clark

Shugaban kungiyar Pan Niger Delta Forum, PANDEF, Edwin Clark, a ranar Alhamis, ya gargadi Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da kada ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Advertisement

Clark yace kamata ya yi Tinubu yaje ya huta duk da cewa ya fito daga yankin da ya fi kowane zamani a Najeriya game da takarar 2023.

Da yake gabatarwa a shirin a gidan talabijin na Arise TV, dattijon yace ya gwammace ya zabi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasar Najeriya.

Advertisement

Clark ya bayyana Osinbajo a matsayin mutum haziki wanda ke da abin da ya kamata ya mulki Najeriya a 2023.

A cewar Clark: “Ban san Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa ba. Ni uba ne a gare shi kuma bai sanar da ni game da irin wannan nufi ba.

“Kudu maso yamma su ne mutanen da suka fi kowa ilimi da wayewa a Najeriya, amma Tinubu ya je ya huta. Ban da Igbo, zan zabi mataimakin shugaban kasa; mutum ne mai hankali.

Sau nawa muka taba jin Tinubu yana magana a kan al’amuran kasar nan ko yana sukar masu mulki?”

A kwanakin baya ne Tinubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa burinsa na rayuwa.

Hakazalika, rahotanni sun nuna cewa nan ba da jimawa ba Osinbajo zai bayyana aniyar sa.

Sai dai mataimakin shugaban kasar ya musanta wadannan rahotannin.

Advertisement