Siyasa

2023: Tinubu ne zai lashe zaben fidda gwani na APC – Sanata Adeniyi

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress APC a jihar Ekiti, Sanata Tony Adeniyi, yace tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Adeniyi wanda yayi magana a Akure a lokacin da yake jawabi ga yan kungiyar Tinubu Hope for Nigeria Vanguard, yace wasu fitattun yan Arewa ne suka fara yunkurin neman shugabancin Tinubu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa babu wani dan takara da zai iya kayar da Tinubu a jihohin Kano, Borno, Katsina, Sokoto, Kwara da sauran jihohin Arewa.

A cewar shi: “Wasu yan Arewa ne suka kira mu don mu fara tallata takarar shugaban kasa na Tinubu. Haka muka fara ajandar Kudu maso Yamma.

“Tinubu yana da hangen nesa da kishin cigaban Najeriya. A siyasa ba abu ne mai sauki a tsaya a dauki matsayi ba. Asiwaju Tinubu yayi abubuwa da yawa don shiryawa wannan rana.

“Tinubu yana can. Ya kasance yana zagawa. Babu wanda zai kayar da Tinu a Kano, Borno, Katsina, Sokoto da Kwara. Zai samu kashi 100 na kuri’un daga wadannan wuraren.”

Advertisement