Siyasa

2023: Saraki, Tambuwal da Ortom zasu fuskanci shari’a kan barin APC

Masu iya magana sun ce tsiya ke tayar tsohon bashi – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya na shirin kalubalantar canja jam’iyyar da gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, Samuel Ortom na jihar Benue da kuma Godwnin Obaseki na jihar Edo suka yi zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar The Nation ta habarto cewa wannan yunkurin na jam’iyya mai mulki, APC, ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun Tarayya dake da zama a Abuja ta yanke na tsige Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi daga kujerar shi ta gwaman jihar saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan an zabe shi a karkashin tutar jam’iyyar adawa PDP.

Jam’iyyar APC na ganin za ta fi cin riba matuka idan har aka aiwatar da irin wannan hukuncia kan gwamnoni da wasu shugabannin PDP da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar APC kuma daga baya suka tsallaka zuwa PDP.

Advertisement

Aminu Tambuwal, Sokoto, Samuel Ortom, Benue da Godwin Obaseki na jihar Edo duk sun sauya sheka zuwa PDP bayan an zabe su a karon farko karkashin inuwar jam’iyyar APC a lokuta daban-ban.

An nakalto cewa za’a hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki a cikin sabuwar karar da ake shirin shigar nan gaba kadan.

Jam’iyyar APCn na neman a haramtawa Saraki yin takarar kowane irin mukami na tsawon shekaru talatin 30, saboda ya sauya sheka bayan lashe zabe a karkashin jam’iyyar tutar jam’iyyar APC a wancan lokacin.

Haka zalika, da take tabbatar da cigaban da aka samu bayan tsige Gwamna Umahi, wata majiya a jam’iyyar APC mai mulki a Abuja, tace an sanar da tawagar lauyoyi kan batun shigar sabuwar karar, amma matakin ya samu tsaiko saboda rikicin shugabanci da ya dabai-baye jam’iyyar mai mulki a cewar rahoton jaridar Thisday.

Majiyar tace;

“Da gaske ne jam’iyyar APC na shirye-shiryen daukaka kara a kan wasu gwamnoni da suka sauya sheka daga jam’iyyar mu ta APC zuwa PDP.

“Zan iya tabbatar maku cewa jam’iyyar mu ta kammala tattaunawa da tawagar lauyoyin mu, da zaran an sulhunta rikicin shugabancin jam’iyyar dake gudana a yanzu, muna sa ran daukaka wannan karar daga kowane lokaci.”

Advertisement