Siyasa

2023: Sabon rikicin APC baya rasa nasaba da neman yikitin takarar shugabancin ƙasa

A fili take rikicin Jam’iyar APC mulki na cigaba da daukar wani sabon salo, takanin bangaren mai neman takarar shugabancin Najeriya, kuma shugaban jam’iyyar a matakin ƙasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma shugaban rikon na jam’iyar Kuma gwaman jihar Yobe Mai-Mala Buni.

A fili take Tinubu na ganin gwamna Mai-Mala Buni a matsayin barazana muradin shi na neman tikitin APC a 2023.

Mutane da dama na ganin ire-iren waɗannan dalilai da makamantan su sune suka sanya bangarorin biyu basa ga miciji da juna a jam’iyar ta APC.

Advertisement

Yanzu haka a fili take dangantaka tsakanin bangarorin biyu tana cigaba da tsami, inda wasu gwamnanoni ke goyawa gwamna Mai-Mala Buni baya, yayin da shima jigo a jam’iyar APC Tinubu yana da goyon bayan gwamnoni a Arewa kamar irin su Abubakar Sani Bello na jihar Neja, da kuma gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement