Siyasa

2023: Nine mutumin da ya fi dacewa ya kwace mulki daga hannun APC, Wike ya bayyana takarar shugaban kasa

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani na jam’iyyar da za a yi a watan Mayun 2022.

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci takwaran shi na jihar Benue, Samuel Ortom, a gidan gwamnati da ke Makurdi.

Gwamnan yace shi ne ya fi kowa cancantar kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekara mai zuwa (2023).

Yace: “Don kawar da APC daga mulki, ni ne wanda zan iya gaya musu ya isa. Dole ne mu dauki wannan mulki kuma a shirye nake in karba wa PDP. Allah yana tare da mu shi yasa APC ta cigaba da gazawa kullum.”

Wike  ya kuma caccaki yan siyasar da suka fice daga PDP a lokutan wahala.

Gwamnan ya kara da cewa: “Na tsaya takarar wannan jam’iyya. Na yi aiki da wannan jam’iyyar tun 1998. Ba ni da inda zan tsaya don haka ne duk wani abu da ya faru da wannan jam’iyya na dauka da kaina. Ban taba tuba ba.

Back to top button