Siyasa

2023: Najeriya na zubar da jini a karkashin APC, dole ne PDP ta karbi mulki – Wike

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, a ranar Laraba, yace munanan ayyukan da jam’iyyar APC mai mulki ta yi a jihar Filato da ma a matakin kasa, yasa babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta samu sauki wajen kwato mulki a 2023.

Hakazalika ya koka kan cewa kasar nan na zubar da jini, kuma jihar Filato bata tsira ba, yana mai cewa dumbin kalubalen da ake fama da su a halin yanzu da suka hada da rashin tsaro, fatara, kunci, da dai sauransu ba su san addini ko yankin siyasa ba.

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da yan jarida a wajen wata babbar kotun Jos, inda ya zo domin marawa tsohon gwamnan jihar, Sanata Jonah Jang, wanda ke fuskantar shari’a bisa zargin zamba baya.

Advertisement

Ana tuhumar Jang ne tare da Yusuf Pam, wani tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar kan zargin zamba ta ₦6.3bn da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gabatar a gaban kotu.

Advertisement