Siyasa

2023: Jonathan ya goyi bayan takarar Bala Mohammed ta shugaban kasa

Hoto: Gwamna Bala Mohammed, Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya goyi bayan aniyar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi na shugaban kasa gabanin zaben 2023.

Jonathan, yayin ganawar shi da Mohammed a gidan shi, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Gwamnan, wanda ya yi Ministan Babban Birnin Tarayya, a gwamnatin shi, ya cancanta kuma ya mai da hankali ne wajen jagorantar Najeriya.

Idan kana nan (a matsayina Shugaban kasa), to ina da da, kowane uba yana son dan shiya girma,” inji Jonathan.

Advertisement

Jonathan ya bayyana cewa aikin shi ne ya tallafawa wadanda suka yi aiki tare da shi a lokacin da yake shugaban kasa.

“Ku da kuka yi aiki tare da ni, ya zama wajibi na in tallafa muku. Mu iyali daya ne. Abu mai kyawu zai same mu,” in ji shi.

A cewar tsohon shugaban kasar, Mohammed kwararre ne da mai da hankali sosai kuma “da ikon Allah, tare da goyon bayan ‘yan Najeriya da Allah, zai zama shugaban Najeriya.

Advertisement