Siyasa

2023: Ina da tabbacin samun tikitin takarar a PDP – Inji Atiku bayan ganawa da Obasanjo

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi alfahari da cewa yana da yakinin cewa zai samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.

Atiku  ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da yan jarida jim kadan bayan ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidan marigayin dake Abeokuta, jihar Ogun.

Arewa Times Hausa ta ruwaito cewa Atiku ya isa dakin karatu na Olusegun Obasanjo, Abeokuta don ganawa da tsohon shugaban makarantar shi a siyasance.

Advertisement

A lokacin da yake amsa tambayoyi daga yan jarida bayan taron, mai fatan shugaban kasar ya bayyana cewa ba ya shakkar samun tikitin jam’iyyar PDP, yana mai tambaya cikin kakkausar murya “Shin na taba kasa samun tikitin?”

Advertisement