Siyasa

2023: Dalilin da yasa ba zan iya ƙin goyawa Tinubu baya ba – Sarkin Katsina

Sarkin Katsina, Dr. Abdulmuminin Kabir Usman, ya ce babu yadda za’a yi ya sabawa burin shugaban kasa na Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, duba da dadewar dangantakar shi da Masarautar shi wadda a cewar shi, tun kafin hawan shi karagar mulki.

Advertisement

Usman ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Arewa Organizations Movement for Tinubu 2023 karkashin jagorancin Sanata Abu Ibrahim.

Sarkin yace zai duba muradin siyasar shugaban jam’iyyar APC ta kasa, inda zai bada shawarwari, gudunmawa da gyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Advertisement

Yace: “Za mu duba duk wani yunkuri da yake ciki, inda za mu goyi bayan shi, inda ake bukatar goyon baya kuma za mu gyara inda ya dace. Na san Tinubu lokacin da yake gwamna a lokacin da nake hakimin gunduma kuma ya taimake ni ta hanyoyi da dama. Yanzu da nake kan karagar mulki, yana takarar Shugaban kasa, ku gaya mani dalilin da yasa zan yi watsi da shi.

To, wannan mutumin da kuka kawo, Tinubu, yana gida a nan, dan kasa ne kuma yayi min sbu mai yawa. Na kasance a Legas makonni uku da suka wuce, na farko tun 1967 kuma na ga yadda Legas ta canza kuma na kammala cewa duk arzikin kasar yana Legas.”

Da yake jawabi tun da farko, Ibrahim, wanda ya jagoranci kungiyar, yace aikin su a ƙungiyar shi ne su nemi albarkar sarki, goyon baya da kuma shawarwarin bullowar burin Tinubu na zama shugaban Najeriya a 2023.

Yace Tinubu yana da cancantar cancanta da kuma abin da ake bukata don mayar da arzikin kasar nan.

Advertisement