Siyasa

2023: Dalilai 2 da zasu sa Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na APC da rata mai yawa

A yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke kara karatowa, ‘yan siyasa da dama a yankin kudancin Najeriya sun bayyana aniyar su ta zama shugaban kasa, musamman ma idan aka samu ra’ayin cewa jam’iyyar APC na da niyyar bada tikitin takarar shugabancin kasar zuwa kudancin kasar domin samun daidaito da adalci.

Sai dai kuma manyan ‘yan siyasa irin su Rochas Okorocha, Dave Umahi, Bola Tinubu, Orji Uzor Kalu, da dai sauran su sun bayyana aniyar su, kuma dukkan su suna da kyakykyawan damar lashe zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, musamman a lokacin da yan jam’iyyar APC suka yi alkawarin bada dama ga kowa ya shiga takarar tikitin.

Haka kuma, bisa ga abin da ke faruwa, da alama daka tafi kyautatuwa ga tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, domin akwai abubuwa biyu da ke nuna cewa zai iya lashe zaben fidda gwani da tazara mai yawa.

Advertisement

Wadanne abubuwa 2 ne ka iya sa Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na APC da tazara mai yawa?

Na farko dai an samu manyan ‘yan siyasa da dattawa a APC da suka yi alkawarin mara wa Tinubu baya fiye da sauran, wanda hakan na iya taimaka masa matuka. Bari in tunatar da ku cewa yana da goyon bayan Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da dama, kamar yadda ya gana da wadannan mutanen kwanaki da suka gabata.

Baya ga haka, akwai wani rahoto a makonnin da suka gabata, wanda ya bayyana cewa, gwamnonin da ba su gaza 13 ne suka yi alkawarin mara wa Tinubu baya ba, tare da wasu dattijai da dama, wadanda suka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya fi kowa takarar shugabancin kasar nan, wanda hakan na iya taimaka masa matuka wajen mamaye abokan hamayyar shi a zaben fidda gwani da nasara da gagarumin rinjaye.

Abu na biyu da ke nuni da cewa Tinubu na iya kayar da sauran ’yan takara a zaben fidda gwanin shi ne irin karfin da ya ke da shi, kuma sananne ne, wanda hakan na iya tayar da hankalin ’ya’yan jam’iyyar APC da dama da ba su son faduwa a zaben 2023 ga mai yiwuwa dan takarar PDP, Atiku Abubakar. wanda ba abu ne mai sauki ba.

Domin jam’iyyar APC ta cigaba da rike madafun iko, ‘yan jam’iyyar na iya kada kuri’ar amincewa ga Tinubu, wanda hakan zai iya ba shi gagarumin rinjaye a zaben fidda gwani.

Advertisement